Hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana zaben jihar Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba.
Yar takarar jam’iyar APC Aishatu Dahiru da aka fi Sani da Binani ta sami 390, 275 inda abokin karawar ta gwamna mai ci Ahmadu Fintiri, na jam’iyar PDP ya Sami kuri’u 421,524.
Yar takarar jam’iyar APC ta lashe kananan hukumomi 15 inda na jam’iyyar PDP ya lashe kananan hukumomi biyar sai jam’iyar NNPP da ta sami karamar hukuma daya