Hukuma mai kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta sanar da cafke wasu matasa uku da ta same su suna sojan-gona da hukumar.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa snine ya bayyana hakan ga manema labarai.
Yace KAROTA ta cafke matasan ne dai-dai lokacin da suke kan aiki akan titin Independence da misalin ƙarfe 2:30 na dare.
Matasan sun haɗa da Lawan Ahmad Habibu da Abubakar Sale Muhd da kuma Shamsu Ibrahim dukkaninsu mazauna garin Kano.
Bayan da Hukumar ta cafke su sai suka shaida mata cewa suna gudanar da aikinsu ne tare da Lawan Ahmad Habibu tsohon jami’in Hukumar wanda tuni Hukumar ta jima da korarsa daga aiki saboda wannan mummunar ta’ada.
Haka, kuma Hukumar na ci gaba da kira ga jama’a musamman direbobi da su guji bayar da na-goro ga jami’an KAROTA wanda hakan ke zubda mutuncin aikinsu.
Tuni dai hukumar ta miƙa su hannun Rundunar ‘Yansanda ta jihar Kano domin ta faɗaɗa bincike tare da ɗaukar matakin gurfanar da su a gaban Shari’a
Daga karshe shugaban Hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su cigaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar na-goro domin ya fuskanci tuhuma.