Ma’aikatar tsaron Faransa ta tabbatar da ficewar rukunin karshe na Sojinta da ke yaki a Mali bayan shafe shekaru 9 suna fatattakar mayakan kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi, ficewar da ke zuwa bayan tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu tun bayan juyin mulkin Soji a bara waccan.
Biyo Bayan rikicin da ya tilasta ficewar Sojin na Barkhane Faransa ta ce rundunar ta sake gina kanta a kasashen makwabta cikin kasa da watannin 6 da taimakon sojojin kawancen masu taimakawa a yaki da ta’addancin.
Sanarwar ta ce Faransa za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin tsaro a yankin Sahel da Tafkin Chadi da kuma hanyar ruwan Guinea don tabbatar da zaman lafiyar nahiyar Afrika.