Kwamitin Kula da Haramtattun gine-gine da aka yi ba bisa ka’ida ba a ƙarƙashin jagorancin Hon. Baffa Babba Dan’agundi ya amince da rushe wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Kwangila.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar KAROTA Nabulusi Abubakar kofar Naisa shine ya bayyana hakan ga manema labarai inda yace6 alummar unguwar ƙarƙashin jagorancin Dattijo Alh. Abubakar Usman ne suka shigar da ƙorafinsu ga Gwamnatin jihar Kano ta hannun Shugaban Kwamitin Kula da gine-ginen da aka yi su ba bisa ka’ida ba Hon. Baffa Babba Dan’agundi.
Bayan binciken da kwamitin ya gudanar ya gano an yi ginin a kan hanyar magudanar ruwa wanda hakan ke zama barazana ga muhallin al’ummar unguwar ta Kundila.
Shugaban Kwamitin Hon. Baffa Babba Dan’agundi ya ce ba za su zuba ido suna gani wasu na amfani da damarsu ta aiki suna cutar da al’umma ba.
Ya ce tuni mai girma Gwamnan ya bayar da umurnin a rushe wannan gini, sannan kwamitin ya ci gaba da sa-ido a unguwar Kwangila domin ganin ba a ci gaba da gine-ginen magudanar ruwa ba.
Baffa Babba ya ce Mai Girma Gwamnan ya bayar da umurnin bincike tare da gano waɗanda suke da hannu wajen bayar da shaidar yin gini a wajen domin ɗaukar matakin ladabtarwa a kansu.
Tuni dai kwamitin ya jagoranci rushe ginin kamar yadda mai girma Gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarni.
A ƙarshe ya ja hankalin al’ummar unguwar ta Kundila da su ci gaba da gyara magudanar ruwa domin gudun samun ambaliyar ruwa a unguwar tasu.