Kungiyar dake wayar da Kan alumma dangane da yin gwaji kafin aure ta jihar Kano, ta Sha alwashin ci gaba da wayar da Kan matasa maza da mata mahimmancin gwaji kafin aure domin samun;ya;ya masu koshin lafiya a jihar Kano da ma kasa Baki daya.
Shugaban kungiyar na jihar Kano, Alhaji Muharazu Adamu ibrahim gizina ne, ya ba da tabbacin hakan a lokacin da kungiyar ta ziyarci makarantun sakandiren yanmata ta yakasai dake birnin Kano da Kuma, ta Dorayi dake karamar hukumar Gwale domin ci gaba da wayar da Kan matasa amfanin yin gwaji kafin aure, domin kaucewa haifar Yara masu dauke da cutar amosanin jini da sauran cututtuka.
Muharazu Adamu yace, kungiyar an kafata ne, karkashin jagorancin matasa masu kishin alummar jihar Kano da Najeriya, kasancewar iyaye suna mutukar Shan wahala idon suka samu Yara masu dauke da cutar amosanin jini, ta fannin aljihunsu da jikinsu, Wanda ba karamar dawainiya bace a garesu ba.
Shugaban kungiyar ya bukaci Gwamnatin tarayya da ta jiha da sauran shugabanni masu rike da masarautun gargajiya da su taimakawa yunkurin kungiyar na ci gaba da wayar da Kan matasa maza da mata amfanin yin gwaji kafin aure domin kaucewa samun Yara marasa koshin lafiya.
Yace akwai bukatar ci gaba da wayar da Kan alumma duba masu dauke da cutar amosanin jini suna mutukar Shan wahala a wannan lokaci na hunturu dake tafe, dole alumma suna bukatar fadakarwa.
A jawabinsa mataimakin shugabar makarantar yanmata dake unguwar yakasai, malam sadik Tijjani, ya nuna mutukar farin cikinsa bisa wannan ziyarar wayar da Kan matasa amfanin yin gwaji kafin aure domin Mata sune wadanda ya kamata a wayarwa Kai domin kaucewa fadawa cikin irin wannan yanayi.
Itama anata jawabin, shugabar makarantar yanmata ta Dorayi dake karamar hukumar Gwale, Halima Imam, ta jaddada aniyarta na baiwa shugabancin kungiyar goyan bayan daya dace domin samun damar cin nasarorin da aka Sanya a gaba a gaba, na wayar da Kan matasa maza da mata amfanin yin gwaji kafin aure.
Daga karshe ta shawarci iyaye da su kasance masu kulawa da lafiyar wadanda suka zo domin Neman Auren yayansu duba da wahalar dake tattare da cutar amosanin jini da sauran cututtuka da ake kamuwa da su ta hanyar auratayya.