Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta ce zata dawo da jami’anta da aka kora ba bisa ƙa’ida ba
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin da zai bincika musabbabin korar jami’an, da kuma dakatarwar da aka yi wa wasu daga cikin jami’an.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Naisa yace Eng. Faisal Ya ɗora wa kwamitin alhakin tantance jami’an KAROTA domin cire na bogi daga cikinsu.
A don haka, ake sanar da waɗan da abin ya shafa da su je Hukumar ta KAROTA don tantancesu ta hanyar tabbatar da gamsassun hujjojin musabbabin korar tasu da kuma dakatarwar.
Kwamitin mai mambobi guda bakwai yana ƙarƙashin jagorancin Mai Binciken Kuɗi na Hukumar KAROTA, Alh. Sadisu Abubakar Yakasai inda aka debar masa wa’adin makwanni huɗu ya miƙa rahotonsa ga Shugaban Hukumar domin daukar mataƙi na gaba.
A ƙarshe ya roƙi kwamitin su yi aiki tsakani da Allah ba tare da nuna siyasa ko sanayya ba