Hukumar hisbah ta jihar kano ta yabawa masarautar gaya bisa

Hukumar hisbah ta jihar kano ta yabawa masarautar gaya bisa gudimmawar da take bawa hukumar domin ci gaban ayyukan addaini tare da samar da zaman lafiya da taimakawa marasa karfi.

Babban kwamandan hukumar sheik Haroon muhd sani ibn sina shine ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da hukumar hisbah ta kaiwa masarautar.

Sheik ibn sina ya bayyana sarkin Gaya a matsayin sa na jagoran al’umma kuma na gabagaba a iyayen Al”umma a jihar kano saboda yadda yake baiwa hukumar da mar data kamata a fannin aikin su na hisbah

Anasa jawabin sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim ya yaba da wannan ziyarar ta hukumar hisbah tare da yaba mata akan irin ayyukanta na kula da harkokin zamantakewar ma,aurata da ma al’umma baki daya don ganin anbi tsari da tarbiyyar addini .

kwamandan hisbah ya roki masarautar data sa baki ta hanyar yin kira ga mawadata dasu taimakawa masu karamin karfi duba da yanayin da ake ciki.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments