Rahoton da hadaddiyar kungiyar masana’antun injuna ta kasar China ta fitar a jiya, ya nuna cewa, jimillar adadin motocin da kasar ta fitar zuwa kasashen ketare a shekarar 2022 ya kai miliyan 3, a cikin adadin, motocin dake amfani da sabbin makamashi sun fi yawa, inda adadin su ya karu da ninki 1.2 bisa na shekarar 2021.
Alkaluman da kungiyar ta fitar sun nuna cewa, adadin motocin dake amfani da sabbin makamashi da aka kera a kasar Sin a bara, ya kai miliyan 7 da dubu 58, adadin da ya karu da kaso 96.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2021, kuma adadin motocin da aka sayar da su a bara, ya kai miliyan 6 da dubu 887, adadin shi ma ya karu da kaso 93.3 bisa dari, kan na shekarar 2021.
Dukkanin wadannan adadi sun kai matsayin koli a tarihi, kuma sun wuce sahun gaba a duniya a cikin shekaru 8 da suka gabata. Kana adadin motocin sabbin makamashi da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen ketare a bara, ya kai kusan dubu 679, adadin da ya karu da ninki 1.2 bisa na makamancin lokacin shekarar 2021.
An yi hasashen cewa, adadin motocin dake amfani da sabbin makamashi da kasar Sin za ta kera, da kuma sayarwa a bana zai karu. (