Hukumar hisbah ta jihar kano ta bayyana al,amarin wata uwa da ake ta yadawa na cewa ta kashe auranta ta auri saurayin yarta da cewa a ilmance ba wani laifi tayi ba.
Kwamandan hisbah na shiyyar karaye malam yahaya Alasan ne yace a musulumce ba,a yarda uwa ta auri Koda tsohon mijin yarta ba ko da su kadai ne suka rage a duniya auren ya haramta a tsakankanin su.
Malam yahaya Alasan yace a addinance wannan baiwar Allah da ta auri saurayin yarta ba wani abun aibu tayi ba matukar ba kauce tayiwa yar ta ta ba ko kuma ta rabu da mujin ta bata gama idda ba dukkan wadannan zasu iya zama laifi a Shari,AR Musulunci
kwamandan yace tun da farko a jawabin wannan Amarya tace ta rabu da uban ya’yanta tayi idda sannan tsohon saurayin yarta bayan da yar’ tace bata son sa kuma da ga baya yace yaji ya gani zai auri uwar tsaohuwar budurwarsa kuma aka yi magana da magabatan ta sannan aka daura auren .
malam yahaya yace a shari’ance Koda manemin uwar ne tana barawara yazo neman aurenta sai yaga yar’ tayi masa to zai iya canzawa ya koma kan yar’ ta babu laifi
Haka zalika koda neman auren yar”yazo kuma uwar bazawara ce to kuma yaga tayi masa to zai iya komawa kanta
.wakiliyarmu Jamila sulaiman aliyu ta ruwaito mana cewa malam yahaya alasan yace ba dai dai bane a ringa yayata abin da ba,a da ilmi a kansa har a ringa ganin tamkar sun tafka wani Babban laifi.