CBN ya sake jaddada waadin daina karban tsoffin kudade daga ranar 31-01-2023
Babban bankin Najeriya CBN ya jaddada kudurin sa na rufe karbar tsoffin kudaden 200, 500, da kuma 1000 daga ranar 31-01-2023
Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele shine ya tabbatar da hakan a wani sakon faifen video da ya saki a shafinsa na Twitter a yammacin Jiya Asabar.
Emefiele yace babu gudu babu ja da baya ka batun daina amfani da tsofaffin takardun Naira 1000 da 500 da kuma 200 kamar yadda yake a tsare.
Emefiele ya bukaci al’umma da suyi watsi da jita-jitar da ake yadawa na cewa CBN zai kara waadin
Kazalika ya roki yan Najeriya da su yi masa uzuri duba da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari shine ya tabbatar da wannan wa’adi.