Wani bincken kimiyya da aka gudanar ya nuna cewa idan mutum ya wuce awa 4 a cikin jirgi musamman wanda shekarun sa suka haura 50 daya a mutum dari shida zai iya fuskantar matsalar daskarewar jini da ake kira da Deep Venus Thrombosis a turance.
Hakan fito ne daga bakin Jami’i a ma’aikatar lafiya ta Najeriya kuma shugaban likitoci dake kula da maniyata a Hukumar Alhazai ta kasar(NAHCON) Dakta Sa’idu Ahmad Dumbulwa a lokacin ya yake zantawa da Saashen Hausa na VOA.
Dakta Sa’idu Ahmad yace hakan yasa suka bullo sabbin hanyayi da kuma shawarwari da dasu taimaka wajen tabbatar da lafiya maniyatan.
Hanyoyin sun hada da Sanin tarihin lafiyar maniyata musamman ‘yan sama da shewkara 50, Saka kaya da takalma wadanda basu da matsi, tabbatar da cewa akawai ma’aikatan lafiya a jiragen dake jigilar maniyata, da kuma hada gwiwa da ma’aikan jirgin don tsarin wajen zama da tabbatar da akwai duk wasu magungunan da ake bukata a cikin jirgi.
Dr. Sa’id ya kara da cewa sun kuma dauki mataki na wayar da kan Maniyatan a harshen Hausa, Turance, Yoruba da kuma Pigin kan irin matakan daya kamata su dauka don kare aukuwar wannan matsala da suka hada da motsa jiki a cikin jirgi bayan zaman akalla awa biyu.
Idan dai za’a iya tunawa an fara jigilar Alhazai a Najeriya zuwa kasa mai tsarki ne a ranar 25 ga watan Jiya, kawo yanzu akalla mutum 30,000 ne suka isa kasar saudiyya