Kungiyar hadin gwiwa ta mafarauta da yan banga na ci gaba da samun nasara a fafatawar su da ‘yan bindiga masu tayar da kayar baya a jihar Taraba.
Daga Walid Y Hari.
Yayin da rashin zaman lafiya ke ci gaba da addabar wasu yankunan arewacin Najeriya, wasu al’umomi a jihar Taraba sun dauki matakin shawo kan lamuran tsaro, ta hanyar hada taro don daukar nauyin mafarauta su tunkari lamarin.
Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar ‘yan bindiga dake kai wa al’umomin yankunan hare-hare, baya ga haddasa asarar rayuka, su kan kwashi dukiya ko barnatawa tare da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.