Cibiyar al-mutasaddikun charity foundation ta horas da marayu sanao’in dogaro da kai kuma ta basu jari

An bayyana Tallafawa marayu a matsayin  abu ne da yake samar da gwaggwaban lada da kara yalwar arzikin,  don haka ya zama wajibi ga Al’umma su himmatu wajen tallafawa marayun da abubuwan da Allah ya hore musu.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin jawabin  Malama Zainab Sheak Jafar Muhamud Adam ta gabatar  a wani taro da Cibiyar AL-MUTASADDIDIKUN CHARITY FOUNDATION ta  gudanar na yaye dalibai marayu da aka koya musu sana’o’i tare da basu jari a dakin taro na Hajiya Hajara Buhari dake Gwauron Dutse.

A yayin taron Wakilin AKSAM MEDIA Kabiru Muhammad Getso ya rawaito cewa Wasu daga cikim marayun da aka koyawa Sana’a da basu tallafi sun bayyana farin cikin su da godiya ga Shugabar Kungiyar Hajiya Ummi Amunu yusif.

Itama a nata bangaren shugaban kungiyar ta ALMUTASADDIQUN CHARITY FOUNDATION Hajiya Ummi Aminu Yusuf ta bayyana dalilin da yasa suka fito da wannan tsari na koyar da marayu Sana’a da muhimmancin tallafawa marayu tare da kira ga masu hannu da shuni da su cigaba da bada gudummuwa wajen tallafawa irin wadannan kungiyoyi don cigaba da irin wannan ayyukan alkhairan

Kana taron ya samu halaltar manyan malamai da ke cikin da wajen  jihar kano

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments