Sojojin jamhuriyar Niger 3 sun mutu, sanadiyyar hadarin jirgin sama a filin jirgin sama dake Niamey, babban birnin kasar a jiya Litinin.
Wata sanarwa da ma’aikatar tsaro ta Niger ta fitar, ta ce lamarin ya auku ne a lokacin da jirgin soojojin mai saukar ungulu ke kokarin sauka a kan titin tashi da saukar jiragen soji na filin jirgin saman kasa da kasa na Diori Hamani da misalin karfe 10:40 na safiyar jiya.
Dukkan sojoji 3 dake cikin jirgin sun mutu, duk da kokarin da ma’aikatan ceto suka yi na shawo kan gobarar da ta tashi. Sanarwar ta kara da cewa, nan take aka kafa kwamiti domin binciken musabbabin lamarin.