Gwamnatin ta gano bututaye 58 da ake satar danyen Man fetur a jihohin Rivers da Delta

An lalata karin wasu matatun mai 58 ba bisa ka’ida ba a jihohin Bayelsa da Delta na Najeriya, kasa mai mafi arzikin man fetur da iskar gas a nahiyar Afrika.

Jami’in tsaro na Delta, Ekpemupolo Tompolo ya bayyana cewa an samu ci gaba mai kyau a aiyukan da aka gudanar na yaki da satar mai a kwanakin baya.

Tompolo ya rawaito cewa an lalata wasu haramtattun matatun mai guda 58 da aka gano a jihohin Bayelsa da Delta.

Sakamakon satar man fetur da ake ci gaba da yi a Najeriya, adadin man fetur din kasar ya ragu daga ganga miliyan 1.8 a rana zuwa ganga miliyan 1.

Najeriya mai arzikin man fetur da aka tabbatar ya kai kusan ganga biliyan 37, tana da kashi 3.1 cikin 100 na man fetur din duniya.

Najeriya wacce ke cikin kasashe 15 da ke kan gaba wajen hako danyen mai, ita ce kasa ta 8 da ke da arzikin man fetur a duniya sannan ta 6 wajen fitar da mai zuwa kasashen waje.

An bayyana cewa za a iya hako sama da ganga miliyan 1.5 na danyen mai a yankin Rivers da Delta, inda ake da rijiyoyin mai na kasar, amma ba za a iya amfani da akalla ganga dubu 500 ba saboda zagon kasa da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi, da kuma rikice-rikice da sace-sacen mutane.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments