Gwamna Dakta Abdullahi umar Ganguje khadimul Islam ya jaddada aniyarsa na tallafawa alummar jiharnan da kayan abinci domin saukake musu radadin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon sauya fasalin kudi da babban bankin kasarnan ya yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin gangamin yakin neman zabe na jamiyyar Apc wanda ya gudana a karamar hukumar tsanyawa da ke nan kano.
Gwamnan ya bayyana cewar muddin jamiyyar su tayi nasarar lashe zabenta a wannan shekarar to wahalhalun da alumma suke fama dasu Zasu zama tarihi.
Shima anasa bangaren Dan takarar Gwamna a Jamiyyar Apc kuma mataimakin Gwamna a tutar jamiyyar ta Apc Dakta nasiru yusif Gawuna yayi alkawarin zuba kudi kimanin sama sama da naira miliyan hudu domin farfado da dam din watari wanda ya zagaya kananan hukumomi uku na jihar nan.
Ya kuma yiwa alummar yankin alkawarin cewar muddin suka zabe shi zai bijiro da managartan tsare tsare da Zasu amfana.
Shima anasa bangaren dan takarar mataimakin Gwamna a jamiyyar Apc Alhaji Murtala sule garo kira yayi ga babban bankin kasarnan kan yayi kokari wajen rage wa wahalhalun da suke fama da shi na karanci sabbin kudade a hannayensu
Shima anasa bangaren dan takarar sanatan kano ta tsakiya Alhaji Nadau Jibrin maliya ya jaddada aniyarsa na ganin an fara aikin madatsar ruwa ta kogin watari nan da makonni kadan masu zuwa.
Wakilinmu na ofishinsa mataimakin gwamnan jihar Kano shehu Suleiman Sharfadi ya ruwaito cewar taron ya samu halartar kwamishinoni da dama da manyan jamian gwamnati da kuma sauran yan takara na jam’iyyar Apc.