- Daga Sadik Lamin Hassan
Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da gaggauta bude kananan hukumomin Gummi, Anka da Bukkuyum, da kuma dukkan garuruwa, tituna da kasuwanni da gwamnatin ta rufe kwanan nan saboda tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar.
Sanarwar mai dauke da Sa hannu kwamishinan yada labaran jihar Ibrahim Magaji Dosara, inda tacigaba da cewa.
Amincewar ta biyo bayan rahotanni na musamman da aka samu daga al’ummomin da abin ya shafa.
Gwamnati ta kuma janye takunkumin da ta sanya wa harkokin siyasa a jihar.
Sai dai ana shawartar jama’a da su rika gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada, domin gwamnati ba za ta amince da duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da jami’an tsaro ke samu a yanzu haka.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin mai girma Hon (Dr Bello Mohammed Matawallen Maradun, Shatiman Sokoto) ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata na al’ummar jihar.
Snarwar taci gaba dacewa gwamnatin zata tabbatar wa al’ummar jihar jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ ummar jihar.