Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar shekarar Musulunci Adeleke,
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Yuli,
ya ce an bayar da hutun ne domin shigowar shekarar 1445 bayan Hijirah A cewar sanarwar, gwamna Adeleke zai jagoranci wani fareti na musamman tare da al’ummar Musulmai a jihar
Kamar yadda jaridar vanguard ta ruwaito ta tabbatar, da cewa babban sakataren ma’aikatar cikin gida da ayyuka na musamman ta jihar, Mudashiru Oyedeji, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar