Daga Sadik Lamin Hassan.
Manyan jami’an kungiyar Tarayyar Turai guda biyu sun taya Rishi Sunak murna kan shirin zama sabon firaministan kasar Birtaniya na gaba bayan lashe kujerrar shugabancin jam’iyyar Conservative mai mulki tare da fatan nasara kan iya daidaita lamuran kasar.
Manyan jami’an aun hadar da Charles Michel shugaban majalisar gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai tare da Roberta Metsola shugaban majalisar dokokin Turai.
Shi dai Rishi Sunak wanda zai zama sabon firaministan Birtaniya ya kasance tsohon ministan kudin kasar, kuma zai zama firaminista na biyar cikin shekaru shida da suka gabata, abin da ke nuna irin tsaka mai wuya na siyasa da aka shiga a kasar ta Bi rtaniya.