Daga Sadik Lamin Hassan.
‘Yan sanda a Kenya sun kashe wani shahararren dan jaridar Pakistan dake buya a kasar, saboda motar da ya ke tafiya a ciki ta ki tsayawa a wani wurin binciken jami’an tsaro a kusa da birnin Nairobi.
Mahukunta a kasar Sun sanar da cewar kisan nasa kuskure ne, saboda motarsu ta yi kama da wadda ake zargi da sace yaro kuma ana nemanta ruwa a jallo.
Arshad Sharif mai shekaru 50 da haihuwa, yana buya ne a kasar Kenya, bayan tserewa barazanar kama shi a watana Yuli, saboda sukar rundunar sojin kasar sa dake kudancin Asiya mai karfin iko.
‘Yan sandan Nairobi sun sanar da cewar, Sharif ya mutu ne sakamakon harbinsa a kai jiya da daddare, lokacin da motar da ya ke tafiya a cikinta da dan uwansa Khurram Ahemed ta shige a guje ba tare da tsayawa a inda jami’an tsaro ke binciken ababén hawa a kan babban titin Nairobi zuwa Magadi.