Hukumar zaɓe a Turkiyya ta sanar da zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, Mista Erdorgan ya gaza samun kashi 50 na ƙuri`un da za su ba shi nasara.
Shugaban hukumar zaɓen ƙasar Ahmet Yener, ya ce za a gudanar da zagayen zaɓe na biyu ranar 28 ga watan Mayu, wato mako biyu mai zuwa kamar yadda doka ta tanada.
Ahmet Yener ya ce sakamakon zagayen farko na zaɓen ya nuna cewa Shugaba Erdogan ya samu kashi 49.51% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Shi kuwa, babban jagoran ‘yan adawar ƙasar, Kemal Kilicdaroglu, ɗan takarar gamayyar jam’iyyun adawan Turkiyya, ya samu kashi 44.88% na ƙuri’un.