Duda rashin jituwa dake tsakanin Atiku da Wike PDP ta fitar da inda zata fara zuwa yakin neman zabe

Babbar Jam’iyar adawa ta PDP ta bayyana ranar Laraba mai zuwa a matsayin Rana da zata fara fita domin yakin neman zabe.

Jam’iyar bata yi laakari da barakar dake cikin ta ba inda tace zata fara gudanar da dukkan shirye-shiryen da tayi na fita yakin neman zabe daga ranar 28-09-2022.

Sakataren yada labarai na jam’iyar,  Debo Ologunagba, shine ya bayyana hakan ga manema labarai.

Daga bangare guda kuwa wasu kusoshin jam’iyar irin su gwamna Nelson  Wike,  da takwaransa na  Oyo, Seyi Makinde, da tsohon Ministan yada labarai, Prof. Jerry Gana,  da Chief Bode George da wasu jigajigan jam’iyar sun sanar da raba gari da tafiyar Atikun.

 

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments