An bukaci al’ummar jihar Kano da su jajirce wajan baiwa hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA hadin kai na kai karar jami’an hukumar masu ketare iyakar aiki.
Bukatar hakan ta fito daga bakin shugaban hukumar ta KAROTA Honourable Baffa Babba Danagundi a lokacin da yake jawabi ga manema labarai.
Baffa yace hurumin hukumar sa shine ta kama mai laifi ta gurfanar da shi a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.
Ya ja kunnen jama’a da su Kaucewa biyan tara a hanun yan KAROTA idan suka kama ku da goyon biyu a mashin mai kafa biyu
A karshe ya bukaci masana doka da su jajirce wajan wayar da kan mutane akan lamarin da ya shafi doka