Darikar kadiriya ta nada wani sabon Mukaddami

Shugaban darikar kadiriyya na yammacin kasashen Afrika Shek karibullah Nasiru kabara yaja hankalin mukaddami nuraddin Dahiru umar kan yayi koyi da halayen mahaifinsa wajen ilmantarwa da kuma dabbaka harkokin addinin musulunci a ma jiha da kasarnan baki daya.

Shugaban darikar na nahiyar Afrika ta yamma Shek karibullah Nasiru kabara ne ya yi wannan Jan hankalin yayin Nada malam Nuraddin Dahiru umar a matsayin sabon mukaddami wanda zai rika kulawa da harkokin addinin musulunci a unguwar soron dinki wanda ya gudana a gidan Shugaban darikar dake nan kano.

Shugaban darikar na bayyana cewar marigayi malam Dahiru soron dinki fitaccene kuma jajirtaccen malami ne da kare rayuwar sa wajen hidintawa addinin musulunci wanda hakan ta sanya ya zabo dansa malam nuraddin Dahiru domin ya nada shi a matsayin sabon mukaddami wanda zai Maye gurbin mahaifinsa.

Ya kuma bayyana cewar daga cikin ayyukan mukaddami shi ne koyarwa, ilmantarwa da horas da matasa wajen ambaton Allah da kuma neman yarda da neman kusanci Allah subhanahu wataala.

Daganan sai yayi wa sabon mukaddamin adduar samun damar nauyin da ya rayata a wuyansa tare da yi masa fatan alkhairi da kuma neman gafara da rahama ga mahaifinsa malam Dahiru soron dinki.

Shima anasa bangaren sabon mukaddamin malam nuraddin Dahiru umar ya bayyana godiyarsa ga Allah subhanahu wataala bisa wannan nadin da Khalifa darikar kadiriyya Shek karibullah Nasiru kabara yayi masa tare kuma da yiwa mahaifinsa adduar samun rahama a gurin Allah, inda kuma ya roki Allah ya yi riko da hannunsa wajen kwatanta halaye da dabiun mahaifinsa.

Ya kuma yi godiya GA Khalifa darikar kadiriyya bisa wannan amana da aka dora masa, inda kuma yayi kira jagorori da kuma yan uwansa da aka dora wannan amana akan su kan su daure su sauke wannan nauyi da aka dora musu.

Daga karshe yayi alumma fatan alheri bisa samun dama da suka yi wajen halartar taron kaddamar dashi a matsayin Halifan mahaifinsa tare da yi musu fatan komawa gidajen su lafiya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments