Fitaccen mawakin nan da ke sharafi a wannan zamani, Hamisu Breaker ya musanta zargin da ake yi na cewa shi ne saurayin da jarumar nan Rukayya ta ce ya juya mata baya kan soyayyarta da shi.
Rukayya wadda aka fi sani da Rakiya Musa dai ta bayyana a cikin shirin da fitacciar jarumar fina-finan hausa Hadiza Gabon ke gabatarwa a tasharta da ke saman shafukan yanar gizo, inda ta bayyana yadda lamarin soyayyarta da wani bawan Allah da ba ta fadi soanashi ba sai dai yadda ta bada labarin abin da tausayawa da kuma kallon saurayin a matsayin wanda bai kyauta ba.
Wannan labari na ta ne ya dauki hankullan masu amfani da shafukan sada zumunta inda wasu suka rinka zargin ko fitaccen mawakin ne Hamisu Breaker? Saidai shi Breaker din bai yi shiru da bakinsa ba domin kuwa ya saki wani sako a saman shafinsa na Facebook kamar haka
“Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lfy dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan batun da yake ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar Asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tayi hira da ita wasu mutane na cewa wai dani tayi soyayya kuma har na juya mata baya Sam Sam wanna maganar ba haka take Hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai Mutunci.” Inji shi.