Babbar Jam’iyar adawa a Kano APC ta bayyana shirin ta na zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana Abba kabir Yusuf na jam’iyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kano
Jam’iyar ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun ta na jiha Kano Ahmad Aruwa.
Aruwa yace duk da Dan takarar gwamna na jam’iyyar su ta APC Malam Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zababben gwamnan da INEC ta ayyana murna hakan ba zai hana su garzaya wa kotu Dan kalubalantar sakamakon ba.