Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna gamsuwarsa bisa gudumawar da tsofafin daliban Makarantar Firamaren ta Shahuchi suke bayarwa a fannin ilimi a makarantar.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci makarantar domin duba wasu aiyuka da kungiyar tsofaffin dalibai sukayi na gyara wasu ajujuwa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce mutukar tsofaffin dalibai za su rika taimakawa makarantun su hakan zai taimakawa gwamnati wajen ciyar da ilimi gaba a jihar nan dama kasa baki daya.
Haka kuma Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa General Ibrahim Sani Mai ritaya sabo da gudumawar da yake bawa makarantar firamaren ta shahuchi.
A nasa jawabin General Ibrahim Sani ya ce mutukar ya zama gwamnan jihar Kano a zabe shekarar 2023 zai bawa harkokin ilimi fifiko.
Shikuwa da yake nasa jawabin shugaban Makarantar Alhaji Umar Danbaba ya ce makarantar tana kira da gwamnatin data samar musu da jami’an tsaro da yawan malamai da dai sauran kayan aiki na zamani.
Sa hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano
23/11/2022