China ta gina Majalisar Dokoki ga kasar Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ce sabon ginin majalissar dokokin kasarsa da Sin ta tallafa da kudade wajan aiwatar da shi, na daf da mika shi ga Zimbabwe.

Shugaba Mnangagwa ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a harabar ginin, ya kuma yi amfani da damar wajen fayyace ajandar majalissar dokokin kasar, cikin ’yan watannin da suka rage, kafin babban zaben kasar na tsakiyar shekara mai zuwa.

Cikin jawabin nasa shugaban ya jinjinawa kasar Sin, bisa makudan kudaden da ta samar domin gudanar da ginin majalissar dokokin kasar a yankin Mt. Hampden, mai nisan kilomita kusan 25 daga arewa maso yammacin birnin Harare, fadar mulkin kasar

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted