-
Mai Martaba Sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR NCOL ya tunatar da al’umma su cigaba da kasancewa masu tsoron Allah da a zahirinsu da badininsu da kasancewa masu kaunar juna da Kuma kyautata taimakon juna.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne a wajan taron Maukibin Qadiriyya na bana Karo na 72 da Khalifan darikar Qadiriyya na Africa Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara ya shiryawa Kuma aka gudanar Filin taron Kanzul Mudalsam dake Kan titin zuwa Katsina, a cikin birnin Kano.
Mai Martaba Sarkin ya bukaci al’uma su cigaba dayin addu’oi da tausayawa masu rauni dake cikin al’uma.
Yayi Kira ga wadanda Allah ya bawa shugabancin al’uma su dunga saurare da bincikawa ta sahihiyar hanya domin sanin halin da suke ciki domin taimaka musu bisa la’akari da yanayin tsaro da ake fuskanta.
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya godewa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda suka bayar da kyakkyawan tsaro a lokacin gudanar da taron.
Daga bisani ya godewa Malamai da Limamai bisa yadda suke gudanar da addu’oi domin samun Zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.
Sa hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada labarai na Masarautar Kano