Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce kafin Amurka ta koma cikin hukumar raya ilimi, kimiyya da al’adu ta MDD ko UNESCO a takaice, kamata ya yi ta nuna kyakkyawar niyyar biyayya ga dokokin kasa da kasa, domin kuwa ta haka ne kadai za ta samu karbuwa, da goyon bayan mambobin hukumar ta UNESCO.
Mao Ning, ta yi wannan tsokaci ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi mata tambaya game da kalaman sakataren wajen Amurka Antony Blinken, dangane da komawar kasarsa hukumar ta UNESCO.
Mao Ning ta ce wasu rahotanni sun haikaito Mr. Blinken a ranar Laraba na cewa, Sin ce kasa daya tilo mafi bayar da gudummawa ga hukumar ta UNESCO, yayin da Amurka ba ta ma cikin fagen, don haka ya wajaba a sauya yanayin.
A cewar Mao, sau biyu Amurka tana ficewa daga hukumar UNESCO, matakin da ya haifar da matukar koma baya ga ayyukan hukumar.