Aliyu Muhammad ya tsallake rijiya da baya a 2019, saboda makauniyar soyayya daya samu kansa a ciki ta Shugaba Muhammadu Buhar Biyo bayan sake cin zaɓen da Muhammadu Buhari yayi a shekarar 2019,
Aliyu yayi wanka tare da shan ruwan kwata mai warin gaske wanda labarin sa ya Karaɗe ko ina har Ya kusa halaka, dakyar aka ceci rayuwar sa bayan tallafin kuɗi daga wasu mutanen kirki, amma yanzu yan APC sun daina ɗaga wayar sa,
Yace ya ajiye tafiyar ne ba don komai ba sai don ya cigaba da gudanar da rayuwar sa cikin salama bayan ya shiga halin la-ila-hula’i a kowani bangare na rayuwar sa.
Aliyu Sani da aka fi sani da “Aliyu Gayu Na Baba Buhari” yace biyo bayan ficewar da yayi daga tafiyar Baba Buhari, daga yau ya canja sunan zuwa “Ali na Baba Kauran Bauchi”