ranar 9 ga wannan wata na Disamba ne aka mika jirgin saman fasinja samfurin C919 na farko a duniya ga kamfanin China Eastern Airline ko CEA a takaice, kuma a jiya Litinin 26 ga wata, ta fara gwajin zirga-zirgar jirgin na tsawon awoyi 100, domin tantancewa, da kuma tabbatar da tsaron zirga-zirgarsa, da aikin gyara, da sauran ayyuka masu nasaba da inganci.
An yi hasashen cewa, za a fara amfani da jirgin saman fasinjan samfurin C919 na farko a shekarar 2023 dake tafe, bayan da aka tabbatar da cewa zirga-zirgarsa ta dace da ka’idojin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar China.