Hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar China CMSA, ta ce ‘yan sama jannati 3, da suka isa tashar sararin samaniya ta kasar Sin ta kumbon Shenzhou-15, sun yi musayar kama aiki irin sa na farko da rukunin ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 a jiya Juma’a.
A ranar Laraba ne ‘yan sama jannatin Shenzhou-15, suka shiga tashar binciken sararin samaniya ta Sin, inda suka hadu da takwarorin su na kumbon Shenzhou-14, wadanda suke aiki a tashar watanni biyar da suka gabata.
Haduwar rukunonin ‘yan sama jannatin 2, ta kafa tarihin samun karin ‘yan sama jannati zuwa mutum 6, wadanda a karon farko suka yi hadakar gudanar da ayyuka a cikin dakin gwaje gwaje dake tashar.
Yanzu haka dai tasahar sararin samaniya ta kasar Sin ta kafa tarihi na zaman ‘yan sama jannati na tsawon lokaci.
Har ila yau, hukumar CMSA ta ce ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14, sun kawo karshen dukkanin ayyukan da ya dace su gudanar a tashar sararin samaniya ta kasar Sin, kuma za su dawo doron duniyar nan a ranar Lahadi.
Bugu da kari, hukumar ta ce tun a daren ranar Alhamis, tawagar masu bincike da ceto da aka tanada, ta kammala gwajin aiki, domin tabbata da gano wurin saukar ‘yan sama jannatin dake shirin dawowa doron wannan Duniya.