Daga kabiru A Dukawa
Babban bankin Najeriya CBN ya ci alwashin hukunta duk wani bankin yan kasuwa da ya samu ya tare tsoffin takardun kudi na 1000 500 da 200 ba tare da rabawa al’umma ba.
CBN ya bayyana hakan ne a yammacin Jiya alhamis bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki na bankin
A cewar CBN tunda ya rabawa bankunan tsoffin kudade bai ga dalilin da zasu rike kudaden ba bayan al’umma suna cikin bukatar kudade a hannuwan su