Daga Sadiq Lamin Hassan
Shugaba Muhammad Buhari ya snaar da ƙorar shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta Effiong Akwa.
Darektar ƴada labaru na ma’aikatar harkokin Neja Delta, Patricia Deworitshe ce ta bayyana hakan, inda ta ce shugaban ya kuma sanar da kafa sabon hukumar gudanarwa ta hukumar.
Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa za a aike da sunayen sabbin mambobin gudanarwa na hukumar zuwa ga Majalisar Wakilai domin amincewa.
Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya ce ƙorar Effiong Akwa a matsayinsa na shugaban hukumar raya yankin Neja Delta zai kasance nan take farawa daga yau 20 ga watan Oktoban 2022.