Gwamnatin soja ta ƙasar Chadi ta ce mutum 50 aka kashe tare da raunata wasu fiye da 300 sakamakon zanga-zangar da aka shafe yinin Alhamis ana yi don neman mayar da ƙasar mulkin dimokuraɗiyya.
Sabon Firaminita Saleh Kebzabo ya ce wasu daga cikin masu zanga-zangar na ɗauke da makamai.
Cikin waɗanda aka kashe har da jami’an tsaro, a cewar gwamnatin, wadda ta sanar da dokar hana fita a babban birnin ƙasar da kuma wasu garuruwa biyu.
Kazalika ta ce za a ƙaddamar da bincike.
Wani jagoran ‘yan adawa ya faɗa wa BBC cewa za a ci gaba da zanga-zangar har sai an biya musu buƙataunsu.
Rikici ya ɓarke a ranar Alhamis bayan da ‘yan sanda suka yi taho-mu-gama da masu zanga-zangar a N’Djamena, babban birnin ƙasar.
Masu zanga-zangar ta ƙin jinin gwamnati sun yi kaca-kaca da sakatariyar jam’iyyar sabon firaministan ƙasar, Saleh Kebzabo.
Tun farko an tabbar da rasuwar wani ɗan jarida, yayin da aka wuce da waɗanda suka ji rauni zuwa asibitin Union.
Masu zanga-zanga sun ƙona tayoyi sannan suka rufe manyan tituna a babban birnin ƙasar, duk da cewa gwamnati ta haramta zanga-zangar.
Ƙasar Chadi ta kasance kan siraɗi tun bayan kashe shugaba Idriss Deby a watan Afrilun 2021 lokacin da ya ziyarci dakarunsa da ke yaƙi da ‘yan tawaye.
Jami’an tsaro sun far wa kungiyoyin farar hula da ke adawa da mulkin soji lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama a yayin da gwamnatin Faransa ke goyon bayan gwamnatin rikon ƙwarya a Chadi.