Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald da ya shiga tsakanin ‘yan-bindiga da iyalan mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, Malam Tukur Mamu da ‘yan-uwan wadanda aka sace sun tabbatar da sahihancin faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ‘yan-bindiga ke yiwa mutane bugun dawa
Mamu ya ce faifan bidiyon da gaske ne sai dai duk da haka ba zai kara shiga maganar sakin mutanen ba sai idan gwamnati ta sauya salo.
Malam Mamu ya ce cigaba da shiga tsakanin ‘yan-bindigan da kuma ‘yan-uwan wadanda aka sace na da matukar hadari saboda haka ba zai sake tsoma baki ba sai idan gwamnati ta nuna da gaske ta ke yi kuma ta shiga maganar tukuna.
A hirar sa da manema labarai Malam Sani Lawal daya daga cikin ‘yan’uwan wadanda ke hannun ‘yan-bindigan har yanzu ya bayyana cewa ya ga ‘yan-uwan shi a cikin wannan faifai.
Ya ce “ba mu taba shiga halin kunci da damuwa irin na ganin wannan faifan bidiyon ba saboda haka mu na cikin damuwa matuka da irin halin da ‘yan-uwan mu ke ciki a daji”.
Kimanin watanni hudu kenan da sace wadannan mutane a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna kuma har yanzu saura kusan mutane 43 cikin sama da sittin da aka sace da farko.