Gwamnatin Saudi a wani canje-canje da ta gudanar na Ministoci, Mohammed bin Salman ya zama Firayim Minista kamar yadda kamfanin dillacin labarai na kasar ya tabbatar.
Sanarwar tace Ibn Salman ya hau kujerar Mahaifinsa mai shekara 86, kaninsa ya karbi mukaminin Ministan tsaro
Yarima mai jiran gado a kasar Saudi Arabiya, Mohammed bin Salman ya zama sabon Firayim Minista a canjin Ministoci da aka yi.
Gwamnatin Saudi Arabiya ta tabbatar da wannan sauye-sauye da aka yi a gwamnati ta bakin hukumar dillacin labaran kasar a yammacin Talata. Skip Ad Kamar yadda bayanin da aka wallafa a shafin SPA na Twitter ya nuna,
Ibn Salman, ya bar kujerarsa ta Ministan tsaro. Kafin zamansa Firayim Minista, Mohammed bin Salman wanda aka sani da MBS shi ne mataimakin Firayim Minista kuma babban Ministan tsaro.
Khalid bin Salman ya zama babban Ministan tsaro a Yanzu inda ya maye gurin yayan sa Muhammad. Ibn Salman.
Jaridar France 24 tace kusan dai Yariman ne yake juya akalar gwamnatin Saudiyya, wannan mukami da ya samu ya tabbatar da matsayinsa a hukumance