Bayan kwashe watanni uku da fara yaki Zelesky ya bayyana nakasun da ya samu

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi kasar Rasha da aiwatar shirin kisan kare dangi a yankin gabashin kasarsa na Donbas, zargin da ke zuwa dai dai lokacin da yakin kasashen biyu makwabtan juna ke cika watanni 3 da farawa.

Zelensky ya caccaki Rasha ne yayin jawabin da ya saba gabatarwa ‘yan Ukraine kowace rana ta kafar talabijin, inda ya ce hare-haren da Rasha ke kai wa a Donbas ka iya mayar da yankin inda dan adam ba zai iya rayuwa ba, la’akari da aniyarsu ta mayar da garuruwan da ke wajen toka.

A karshen watan Fabrairu shugaban Rasha Vladimir Putin ya aike da sojoji cikin Ukraine, yana mai cewa ya kaddamar da yakin ne domin kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa masu magana da harshen Rashan a kasar ta Ukraine da ke samun goyon bayan kasashen yammacin Turai da Amurka.

A watan Afrilu ne kuma, majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri’ar amincewa da kudurin bayyana mamayar da Rasha ta yi musu a matsayin aiwatar da kisan kare dangi.

A baya bayan nan shugaban Amurka Joe Biden ya ce Putin ya daura aniyar kawar da tunanin kasancewa dan Ukraine daga zukatan ‘yan kasar, ikirarin da Firaministan Canada Justin Trudeau ya yi na’am da shi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments