Babban Kwamandan sojojin kasar Ukraine, Valeriy Zaluhzny yace akalla sojojin gwamnatin kasar 9,000 kasar Rasha ta hallaka tun bayan lokacin da ta kutsa domin mamaye kasar ta Ukraine a watan Fabarairu.
Zaluhzny ya bayyana wannan adadi ne da yake jawabi a wajen wani taro, inda yace tabbas yaran kasar na bukatar kulawa ta musamman, saboda iyayen su sun tafi fagen daga, kuma wasu daga cikin su na daga cikin 9,000 da aka kashe.
Wannan dai shine karo na farko da wani babban jami’in gwamnatin Ukraine ke gabatar da irin wannan koke, duba da cewa basa magana akan nakasun da sojojin kasar ke samu, a cikin watanni shida da suka kwashe suna gwabza yakin.
A watan Afrilun da ya gabata, shugaban kasa Volodymyr Zelensky ya sanar da cewar akalla sojojin gwamnatin kasar kusan 3,000 aka kashe a yakin dake ci gaba da gudana, yayin da wasu 10,000 suka samu raunuka daban daban.
A tattaunawar da suka yi ta wayar tarho ranar Lahadi, shugabannin kasashen Faransa, Jamus, Birtaniya da kuma Amurka, sun sha alwashin ci gaba da taimakawa Ukraine domin kare kan ta daga mamayar Rasha.