Yadda azabtarwar ‘yan bindiga ta sa DPO ‘kashin jini’
Daga Walid Y Hari
Iyalan shugaban ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a Najeriya sun ce jami’in na cikin matsanancin hali a hannun masu garkuwa da shi duk da naira miliyan 7 ta kudin fansa da suka biya.
Wani ɗan uwan DPOn, CSP Sani Gyadi-Gyadi, ya shaida wa BBC cewa an bukaci su biya kuɗin fansa har Naira miliyan 250, wanda ya fi karfinsu don haka suka bayar da abin da ke hannusu amma jami’in bai kuɓuta ba.
Musa Muhammad Gyadi-Gyadi wanda ya kasance babban yaya ga DPOn ya ce a duk lokacin da suka yi waya da ‘yan bindigar suna jin yadda ake lakaɗa wa jami’in duka.
Kuma ya shaida musu cewa azabar da yake ciki ta kai ga yana kashin jini.
Musa Gyadi-Gyadi wanda yayane ga DPO din ya ce sau biyu suna tura kudin fansa, inda da farko bayan bukatar kuɗin fansa na Naira miliyan 250, sai da aka rinƙa bin ‘yan uwa kafin a tara miliyan biyar da aka aike wa‘yan bindigar.
Amma sai ‘yan bindigar suka shaida musu cewa kuɗin abinci ne.