A ranar Lahadi nan ne gidauniya Garewa Charity & Peace ta kai ziyara Asibitin Koyarwar Jami’ar Jihar Kaduna (Barau Dikko) da kuma Gidan Marayu dake unguwar Nasarawa a jihar Kaduna, domin taimakawa marayun da kuma marasa lafiya,
Kimanin marasa lafiya 100 ne aka tallafawa da kudadi naira 5,000, suma marayun maza da mata sama da 47 ne ka basu buhuhunwa shinkafa da main gyada da ruwan roba da kuma kudadi duk da cigaba rayuwarsu
Ton da fari shugaban gidauniyar Alhaji Ibrahim Musa Muhammad Tsafi yace mun yi wannan domin taimakawa al’umma ganin irin yanayin da ake ciki, ya kara da cewa gidauniyar zataci gaba da kai irin wannan ziyarar a jihohin Arewacin kasar da dama kasa baki daya