ASUU ta maka gwamnatin tarayya a gaban kotun ma’aikata.

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za ta tunkari kotun ma’aikata kan lamarin da gwamnati ta gabatar na yiwa kungiyoyin dake kishiyantarta rajista.

Lauyan ASUU, Femi Falana ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Channels Tv, yace kungiyar za ta tunkari kotun ma’aikata domin kai kokenta.

Hakazalika, shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a ranar Alhamis 6 ga watan Okotoba.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta amince da yiwa kungiyoyin malaman jami’o’i na CONUA da NAMDA masu kishiyantar ASUU rajista a yunkurin warware matsalolin yajin aiki.

Rajistar kungiyoyi biyun na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke tattaunawa da ASUU a ci gaba da yajin aikin da kungiyar ke yi.

Yayin bayyana rajistar CONUA da NAMDA, ministan kwadago Chris Ngige ya ce kungiyoyin biyu za su yi aiki kafada da kafada da kungiyar ta ASUU.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments