ASUU: Abin da ya sa aka kasa kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’oi
Daga Walid Y Hari
Watanni shida ke nan tun bayan da ƙungiyar malaman jami’oi a Najeriya ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani kuma har zuwa yanzu, ba a cimma matsaya tsakaninta da gwamnati ba.
Yajin aikin dai ya durƙusar da harkokin karatu a jami’oin gwamnati tare da tilastawa ɗalibai zaman dirshan a gidajensu sai dai wasu sun fara sana’oin hannu domin rage wa kansu raɗaɗin rashin zuwa makaranta.
KToh ko me yake kawo ƙiƙi-ƙaƙa game da batun cimma matsaya? Wani ƙusa a Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya, Barista Abdullahi Jalo dai ya ce wannan matsala ta yajin aikin tana da tushe – ta samo asali ne tun daga yadda aka ƙulla yarjejeniyar farko tsakanin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo da ƙungiyar malaman jami’oin.
Tsohon ƙusan na PDP ya ce matuƙar ana son a kawo ƙarshen yajin aikin nan shi ne a samu daidaito tsakanin ɓangaren gwamnati da na Asuu.
“Ko wane bangare bazai samu yadda yakeso ba sai a hadu a tsakiya ayi hakuri”