Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ta haramta sanya wakar Ado Gwanja ta WARR a gidajen Radiyo da Talabijin na kasar nan.
Hakan na dauke ne cikin wata Sanarwa da hukumar ta fitar mai kwanan watan 06 ga watan Satumba 2022.
Kadaura24 ta rawaito wakar ” Warr ” na daya daga cikin manyan wakokin mawakin wadanda suka shahara a wannan musamman a wajen mata.
Sanarwar da tace an dakatar da sanya wakar ne a radio da Talabijin Saboda wasu kalamai da yake yi a cikin baitocin wakar ta Warr wadanda suka Saba da dokokin hukumar da Kuma al’adar Hausawa.