An shawarci alummar jihar kano da su kasance masu kulawa da tsaftar muhallinsu da abincin da za su ci domin kaucewa kamuwa da cututtuka, musamman yadda cutar zazzabin cizon sauro take addabar alumma a halin yanzu.
Daya daga cikin kungiyar masu rajin ci gaban alummar jihar kano na kasuwar hada Hadar magunguna ta Malam Kato, Alh Hamisu Khalid kwajalawa ne ya ba da wannan shawara a lokacin da yake Karin haske ga manema labarai dangane da yadda zazzabin cizon sauro ya zama ruwan dare.
Yace kamata ya yi alumma su zage damtse wajen tsaftace muhallinsu da share magudanan ruwa a kodayaushe da kiyaye abubuwan ci ko sha da dai sauran nauin kayayyakin abinci.
Hamisu kwajalawa, ya kuma, yi kira Gwamnatoci a matakai daban daban da su fito da wasu sabbin honyoyi da za su tallafawa alumma ta hanyar magance matsalolin zazzabin cizon sauro duba da yadda yake hallaka alumma a kodayaushe.
Hamisu kwajalawa, yace, kamata ya yi a zauna da kwararrun masana a Fannin harkokin kiwan lafiya tare da tabbatar da sahihiyar hanyar da za ta kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro a fadin kasar nan.
Haka zalika, ya shawarci alummar kasar nan da a koma ga Allah subahanahu wata, ala. Wajen kiyayewa da dokokinsa yadda ya kamata da ci gaba da tallafawa mabukata da marasa karfi domin inganta rayuwarsu.