Biyo Bayan juyin mulki da soji suka yi a kasar Burkina Faso tun a watan Satumba a yanzu haka Amurka ta cire kasar daga cancantar damar yin kasuwanci a kasuwannin Amurka a karkashin Dokar Bunkasar kasashen Afrika da Damammaki wato AGOA.
Wasu Kafafen yada labarai na kasar Amurka sun bayyana cewa kasar Burkina Faso ta fice daga dokar kasuwanci na AGOA tun daga ranar 1/01/2023 kasancewar ba ta samu ci gaba a fannin bin doka da oda da dimokradiyya ba.
Za a sanya ido kan ko Burkina Faso za ta samu ci gaba a ababen da ake bukata don aiki da dokar AGOA domin sake samun cancantar damar amfani da dokar.
A ranar 1/01/ 2022 ne Amurka ta cire Habasha, Mali da Guinea daga dokar kasuwanci na AGOA, saboda take hakkin dan Adam da juyin mulki.
Dokar ta bai wa kasashen Afrika 38 damar yin cinikayya ba tare da haraji ba da Amurka.
Ana bukatar kasashen da ke son cin gajiyar dokar AGOA da su cika wasu sharudda kan batutuwan da suka hada da bin doka da oda, kare hakkin dan Adam da dimokradiyya.