Amurka na gab da cimma wata yarjejeniya da Ibrahim Bagudu domin warware wata shari’a a kotu game da dala miliyan 140 da masu binciken Amurka suka ce gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ya sace tare da safarar su zuwa Amurka
Ma’aikatar shari’a ta Amurka da dan ‘uwa gwamnan jihar Kebbi a Najeriya, Ibrahim Bagudu, wanda shi ne babban mai shigar da kara a shari’ar, a ranar Larabar da ta gabata ne suka bukaci a dakatar da shari’ar da ke gudana a wata kotun tarayya da ke birnin Washington.
Bangarorin biyu sun amince da sasantawa ba tare da kotu ba kuma sun yi imanin cewa dan gajeren lokaci zai ba su damar “cimma yarjejeniya ta karshe don warware karar, a cewar takardun kotun.
Kafin ya fara shiga siyasa a matsayinsa na Sanata kuma a yanzu Gwamna, Bagudu ya kasance mai rike da madafun iko ga marigayi Janar Sani Abacha, kafin mutuwar tsohon shugaban a shekarar 1998 ana zargin shi da taimakawa karkatar da biliyoyin daloli da aka sace daga Najeriya.
A cikin wani kuduri na hadin gwiwa zuwa Kotun Koli ta Amurka, bangarorin sun bukaci a tsagaita daga 3 ga Agusta zuwa akalla 9 ga Nuwamba 2022.
Alkalin da ke jagorantar shari’ar, John Bates, ya amince da bukatarsu, amma ya umurci bangarorin da su bayar da cikakken bayani kan tattaunawar nan da ranar 2 ga watan Nuwamba, tare da bayyanawa kotun ko an cimma matsaya ta karshe, ko kuma a ci gaba da dage shari’ar saboda gagarumin ci gaban da bangarorin suka samu a tattaunawar.
Yayin da yake samun kariya daga tuhuma a matsayinsa na gwamnan jihar Kebbi, a baya ma’aikatan binciken Amurka sun taimaka wajen kwato kudaden Abacha da aka sace da aka gano a cikin kamfanonin Bagudu na mai a fadin duniya.