Daga Walid Hari.
Tattalin Arzikin Najeriya da ‘yan kasuwa sun yi asarar sama da Naira Tiriliyan 1 cikin makonni biyu sakamakon matsalar ambaliyar ruwa, kamar yadda wani masani ya shaidawa
Kogi, Benue, Anambra, Niger, Nasarawa da sauran jihohin Najeriya ne ambaliyar ta fi shafa.
An nutsar da gidaje da dama, an yanke katon busasshiyar kasa, an rasa rayuka sama da 80 tare da raba mutane 600,000 da muhallansu a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce matsalar ambaliyar ruwa na sanya radadi mai yawa.
Da yake mayar da martani game da ci gaban a wata tattaunawa kwararre kan hada-hadar kudi/Wealth Management Mista Idakolo Gbolade ya ce “Ambaliya ta baya-bayan nan ta shafi mafi yawan yankunan da ake noma a Najeriya, inda hakan ya shafi wadatuwa, da tsadar kayayyakin abinci “.