Al’ummar karamar hukumar nassarawa na ci gaba da nuna rashin gamsuwar su akan kudurin da wasu daga kansilolin karamar hukumar suka zartas Akan shugaban karamar hukumar ta nasarawa Hon Alhaji AwwAl Lawal Aramposu na yun kurin dakatar da shi da suka ayyana.
Wasu yan asalin karamar hukumar suna ci gaba da nuna kauna ga shugaban duk da sunsan wannan dakatarwar abune Mai wuya domin wani sashe na kansilolin shi kadai bashi da hurumi akan dakatarwar har sai ya samu sahalewar majalisar karamar hukumar da sauran matakai da muddin ba,a cika su ba to ba shakka wannan dakatarwar dai dai take da wasan yara.
Wani jigo a karamar hukumar yace ba bakon Abu bane ace ana takun saka da kansiloli da kuma shugaban karamar hukuma saboda wata bukata ta kashin kansu da suke son cimma sai su tsiro da irin wannan da gangan don cimma muradansu
Jigon Wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce a wannan yanayin akwai yiwuwar kansilolin suna da bukatar samun wata alfarma ko kudi daga shugaban don haka suka tsuro da wannan hanyar da suke ganin ita zata basu cikar burinsu
A cewarsa.wasu matasa da AKSAM MEDIA ta zanta dasu sun bayyana cewa dukkan zarge zargen da kansilolin suka lasafta akan Alhaji Awwal basu da tushe ballantana makama
Hakazalika wani kusa a jam’iyyar ta Apc yace wannan yunkurin bazai yi nasara ba domin Honorable Awwal mutum ne na jama’a kuma Al’ummar yankin suna kaunarsa